1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka na son daliban jami'o'i su yi zanga-zangar lumana

Abdoulaye Mamane Amadou
April 28, 2024

Kwanaki bayan karadewar zanga-znagar da boren goyoyn bayan Falasdinawa a jami'o'in Amurka, gwamnatin kasar na son masu zanga-zangar su yi rika yin bore a cikin lumana.

https://p.dw.com/p/4fH9g
Hoto: AFP via Getty Images

Fadar White House ta Amurka ta yi kira ga masu bore da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a jami'o'in kasar da su rika yin zanga-zangar cikin lumana.

Karin bayani:  An kama fiye da masu zanga-zanga 100 a Amurka

A wata ganawa da manema labarai kakakin ma'aikatar tsaron cikin gidan Amurka John Kirby, ya ce gwamnatin Amurka na mutunta 'yanci da walwalar fitowa yin zanga-zangar da kowa yake da shi, to amma kuma tana Allah wadarai da muggan kalamun kyama da nuna kin jinin Yahuwadawa da ake furtana a yayin zanga-zangar.

A baya-bayan nan dai bore da zanga-zangar nuna goyoyn bayan Falasdinawa ta karade wasu manyan jami'o'in biranen Amurka, ko a waannan Asabar jami'an kwantar da tarzoma sun tarwatsa dandazon masu boren a jami'ar Boston, tare da kama wasu da dama.

Karin bayani: Ya kamata Amurka da Chaina su kasance abokan hulda- Xi Jinping

Ya zuwa yanzu dai hukumomi na cewa an kama fiye da mutane 270 a zanga-zangar.